Birtaniya

Sarauniyar Ingila ta yi martani kan ficewar Birtaniya a Turai

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II REUTERS/Suzanne Plunkett

Fadar sarauniyar Ingila ta Buchingham ta maida martini ga wani rahoto da ya bayyana sarauniya Elizabeth ta biyu a matsayin mai goyon bayan ficewar kasar daga tarayyar Turai, inda ta ce ko kadan babu gaskiya cikin rahoton da jaridar The Sun da ake bugawa a kasar ta fitar. 

Talla

Jaraidar The Sun da ake bugawa a Birtaniya ce ta wallafa a shafinta na farko cewa sarauniyar na goyon bayan ficewar kasar daga tarayyar Turai.

Rahoton da fadar ta ce babu kanshin gaskiya ko kadan a cikinsa, lura da yadda martaba da kimar sarauniyar ta ke ga kowa a kasar, don haka sarauniya ba ta tsoma baki a duk wani zarafi irin na siyasa balle ma ta dau ki bangare.

A cewar mai magana da yawun fadar ta Buchingham, ba wannan ne karon farko da waccen jarida ke rahoton kage ga sarauniyar ba, domin ko a watan Yulin 2015 sai da ta wallafa hoton sarauniya tana yarinya tana jinjina ga 'yan Nazi a shekara ta 1930.

Inji sanarwar dai shekaru 63 sarauniyar ta kwashe tana hidimta wa kowa a kasar kuma ba ta da wani bangare, kowa nata ne, don haka babu dalilin danganta ta da wancen batu.
A ranar 23 ga watan Yuni ne al’ummar Birtaniya za su kada kuri’ar amincewa da kudirin ci gaba da zama a kungiyar ta EU ko kuma a a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI