EU-Turkiya-Girka

Yarjejeniyar Eu da Turkiya kan bakin Haure ta gaza

'Yan gudun Hijira na cigaba da kutsa kai Turai
'Yan gudun Hijira na cigaba da kutsa kai Turai REUTERS/Alexandros Avramidis

Rahotanni daga kasar Girka sun ce yarjejeniyar da Turkiya ta kulla da kungiyar kasahsen Turai na hana baki isa nahiyar Turai ta gaza wajen barin akalla baki sama da 50 isa kasar Girka.

Talla

Kamfanin dillanci labaran Reuters ya ruwaito cewar akalla baki 50 suka tsallaka zuwa Turan duk da alkawarin toshe duk wata kafa da za ta baiwa bakin daman kutsawa zuwa Turai da Turkiya ta yi alkawari dan bata makudan kudade.

Wakilin Reuters ya ce yaga kwale-kwale uku dauke da baki safiyar lahadi da suka isa gabar ruwan Girka.

Kana masu gadi a teku Girka sun rawaito tsinto gawarwaki kanana yara mata biyu a ruwa, wadanda shekarun su ke tsakanin 1 zuwa 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.