Britaniya-Amurka

''Ina nan kan baka ta akan Trump''

Firaministan Britaniya David Cameron
Firaministan Britaniya David Cameron REUTERS/Christopher Furlong/Pool

Firaministan Birtaniya David Cameron yace ba zai janye sukar da ya yiwa dan takarar zaben shugaban kasar Jam’iyyar Republican a kasar Amurka, Donald Trump ba, saboda abinda ya kira manufar sa ta hana Musulmai zuwa Amurka idan ya lashe zaben kasar.

Talla

Cameron ya bayyana matsayin na Trump a matsayin abin takaici, mara kyau da kuma dabbanci, a ganawar da yayi da manema labarai.

Mai baiwa Trump shawara kan harkokin kasashen waje George Papadoulos ya bukaci David Cameron ya janye sukar amma Firaminsitan yace ko gezau baya yi.

'Yan kasar Birtaniya sama da rabin miliyan suka sanya hannu a takardar hana Donald Trump shiga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.