Girka

Mutanen Girka na adawa da sabon tsarin Fansho

Mutanen Girka na zanga-zangar adawa da sabon tsarin Fansho
Mutanen Girka na zanga-zangar adawa da sabon tsarin Fansho REUTERS

Dubban mutanen Girka sun fito zanga-zanga a Athens domin adawa da shirin yin gyran fuska ga tsarin haraji da kuma Fansho a yayin Majalisar kasar ke shirin kada kuri’ar amincewa da sabbin tsare tsaren da masu bin Girka bashi, da suka hada da Tarayyar Turai da Asusun lamuni na duniya suka bukata kafin ganawar da zasu yi a gobe Litinin.

Talla

Shirin dai ya kunshi rage kudaden fansho tare da kara wa ‘yan kasar wani kaso na kudaden da suke bayar wa domin fansho.

Haka kuma kuma za a kara kudaden haraji ga mutanen Girka.

Wannan dai na daga cikin bukatun Asusun lamuni da Tarayyar Turai na tsuke bakin aljihun gwamnati kafin Girka ta samu tallafin kudi euro biliyan 86.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI