Britaniya

Cameron na amfani da salon Trump- Khan

Sabon magajin garin birnin London, Sadiq Khan
Sabon magajin garin birnin London, Sadiq Khan REUTERS/Toby Melville

Sabon magajin garin birnin London Sadiq Khan, ya zargi Firaministan Birtaniya David Cameron da amfani da irin salon siyasar Donald Trump na Amurka don raba kan al’ummar Birtaniya da kuma hana shi samun nasara.

Talla

Kwana guda bayan rantsar da shi, Khan ya yi alkawarin zama magajin garin daukacin mazauna birnin London, bayan ya zargi 'yan jam’iyyar Conservative da kokarin danganta shi da masu tada kayar baya.

Khan ya samu kashi 57 na kuri’un da aka kada inda ya kayar da abokin hamayyarsa Tory Zac Goldsmith, hamshakin attajiri.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.