Girka

Majalisar Girka ta amince da sabbin matakan tsuke aljihu

Mutanen Girka na zanga-zangar adawa da sabbin matakan tsuke bakin aljihu
Mutanen Girka na zanga-zangar adawa da sabbin matakan tsuke bakin aljihu REUTERS/Alkis Konstantinidis

Majalisar Girka ta amince da wasu sabbin matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da suka hada da rage kudaden Fansho da kara kudaden haraji kamar yadda masu bin kasar bashi suka bukata.

Talla

Sai dai kuma ‘yan sanda na ci gaba da arangama da masu zanga-zanga a birnin Athens wadanda ke adawa da sabbin matakan na tsuke bakin aljihu.

A yau ne a Brussels, ministocin kudin kasashen Tarayyar Turai zasu yi nazari akan tallafin da aka ba Girka da kuma sabon bashin kudi karo na uku da kasar ke fatar samu dagaTarayyar Turai da Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF.

Girka za ta samu Karin tallafin kudi kimanin biliyan 86 na Yuro.

Sai dai akwai sabani tsakanin mambobin kasashen Turai da Asusun lamuni na duniya kan matakan da Girka ya kamata ta dauka domin samun Karin tallafi.

Rage kudaden Fansho da Karin kudaden haraji matakai ne da zai taimakawa Girka samun Karin tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI