Faransa

An kai sabon harin ta'addanci a Faransa

Wata motar yan Sandan Faransa yan lokuta da kashe dan bindigan a Magnanville
Wata motar yan Sandan Faransa yan lokuta da kashe dan bindigan a Magnanville MATTHIEU ALEXANDRE / AFP

'Yan Sanda sun ce sun yi nasarar kashe wani mutum da ya hallaka wani jami’in dan Sanda daya da abokiyar zaman sa a Magnanville dake wajen birnin Paris.

Talla

Bayanai sun ce wanda ake zargin ya dabawa Dan Sanda wuka ne a gidan sa, kafin ya kutsa kai cikin gidan inda yayi garkuwa da matar dake zama da mutumin da dan su guda.

Bayan Yan Sanda sun kasa cimma yarjejeniya a tattaunawar da suka yi, sun kutsa kai gidan inda suka kashe shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.