Britaniya

Yakin Nasarar Zaben Raba Gardama Ya Kankama A Britaniya Ana Saura Kwana 3

Fira Minstan Britaniya David Cameron
Fira Minstan Britaniya David Cameron rfi

Kwanaki uku kafin zaben raba gardama a Britaniya  Fira Minista David Cameron ya yi gargadin cewa muddin suka fice daga cikin kungiyar Tarayyar Turai to shakka babu tattalin arzikin kasar ya boni.David Cameron na Magana ne a wani lokaci da masu bukatar ficewar Britaniya daga kungiyar ke zafafa ganin sun yi nasara.  

Talla

Bayan an dan lafa da batun zaben raba gardaman, saboda kisan da aka yi wa wata ‘yan majalisa Jo Cox mai kyamar ficewar kasar daga kungiyar Turai, yanzu haka dai bangarorin dake neman a fice da masu neman kada a fice sun koma yakin neman nasara.

Muddin dai Britaniya ta fice daga kungiyar zata kasance kasa ta farko da ta fice cikin shekaru 60 na kungiyar kasashen Tarayyar Turai.

Fira Ministan  Britaniya David Cameron dake sukan ficewar yace muddin suka fice to kuwa tattalin arzikin Britania zai fuskance matsala.

Hada-hadan zaben raba gardaman dai ya fuskanci hutun kwanaki uku ne saboda mutuwar ita ‘yan majalisa Jo Cox , ‘yar shekaru 41, kisan da ya kasance na farko irinsa tun shekara ta 1990.

Shekaranjiya asabar wanda ake zargi ya kashe ta Thomas Mair ,mai shekaru 52 aka gurfanar dashi gaban kotu, yana ta kururuwa cikin kotun , kuma alkalin kotun ya nemi a ci gaba da tsare shi, amma kuma a samo rahoton likitan mahaukata ko mutumin yana da tabin hankali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.