Birtaniya

Ana ci gaba da cecekuce kan ficewar Birtaniya a Turai

Ficewar Birtaniya ta janyo cecekuce a duniya
Ficewar Birtaniya ta janyo cecekuce a duniya REUTERS/Eric Vidal

Kasashen duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan kuri’ar raba gardamar da al’ummar Birtaniya suka kada bayan sakamako ya nuna cewa, masu goyon bayan ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai sun samu rinjaye.

Talla

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean Marc Ayrault ya jajanta wa Birtaniya kan matakin da ta dauka na zaben ficewa daga kungiyar tarayyar Turai.

Ana sa ran idan anjima shi ma shugaban Faransa, Francois Hollande zai yi na shi toskacin game da zaben da zarar ya kammala ganawa da ministocinsa a yau jumma’a.

Kazalika shugaban Amurka Barack Obama zai zanta da Firaministan Birtaniya David Cameron kan wannan batu kamar yadda fadar White House ta sanar a safiyar yau.

Suma jam’iyyun masu tsattsauran ra’ayi na Turai sun bukaci a gudanar da irin wannan zaben na raba gardama a kasashensu yayin da Marine Le pen ta Faransa ta ce, ya zama dole Faransawa su samu damar kada irin wannan kuri’ar.

Ha kaza dan siyasar nan na Netherland mai adawa da karban baki, Geert Wilders ya ce, ya kamata kasarsa ta dauki irin wannan matakin.

Sai dai minitan harkokin wajen Austria Sebastian Kurz cewa ya yi, ya yi amanna kungiyar tarayyar Turai ba za ta ruguje ba saboda ficewar Birtaniya.

Tuni matakin ya jefa fargaba ga 'yan kasuwa da masu zuba jari, inda kudin Fam ya yi faduwar da bai taba yi a cikin shekaru 31 ba, yayin da hannayen jari suka fadi ganin yadda Birtaniya ta zama kasa ta farko a cikin shekaru 60 da za ta fice daga kungiyar.

Wannan dai ba karamar nasara ba ce ga Boris Johnson da Nigel Farage da Michael Gove, yayin da Firaminista David Cameron ya ce zai sauka daga mukaminsa a watan Oktoba mai zuwa.

A bangare guda, kasashen da suka kafa kungiyar ta Turai sun kira wani taron gaggawa a gobe Asabar don nazari kan matakin da Birtaniya ta dauka na ficewar.

Ministocin harkokin wajen kasashen Faransa da Jamus da Nertherlands da Luxembourg da Belguim da Italiya za su halarci taron na gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.