Birtaniya

Brexit: David Cameron zai yi murabus

David Cameron a 10 Downing Street, London
David Cameron a 10 Downing Street, London REUTERS/Stefan Wermuth

Siyasar Birtaniya ta rikide a yau Juma’a bayan masu da’awar ficewar kasar daga Tarayyar Turai sun samu nasara a kuri’ar raba gardama da aka jefa a jiya. Tuni Firaministan kasar David Cameron ya sanar da zai yi yin murabus.

Talla

Masu son ficewar Birtaniya sun samu nasara da kashi 52 a kuri’ar raba gardama da aka kada a jiya Alhamis. Wadanda ke son ci gaba da zama Birtaniya sun samu kashi 48 na kuri’a.

Matakin murabus din David Cameron ya bude kofar hammayar shugabanci kan wanda zai yi jagoranci a yanayin da yanzu Birtaniya za ta tsinci kanta a ciki.

Tuni dai aka fara ganin tasirin matakin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai na faduwar darajar kudin kasar.

A lokacin da ya ke bayyana yin murabus Firaminista David Cameron da ke yakin dawwamar Birtaniya a kungiyar Turai ya ce a watan Oktoba za a zabi sabon shugaba.

“Mataki ne da ya dace sabon Firaministan ya yanke shawarar bin tsarin dokokin da suka dace na ficewa Kungiyar Tarayyar Turai” a cewar Cameron.

Sannan Cameron ya ce kofar shi a bude ta ke domin bayar taimakon da ya dace ga gina sabuwar Birtaniya.

Babu dai tabbas kan makomar Tattalin arzikin Birtaniya a yau Jum’a a yayin da ake muhara kan tasirin ficewar birtaniya ga matsaloli da dama musamman rashin ayyukan yi.

Jeremy Corbyn shugaban jam’iyyar Labour kuma wanda ke da’awar zaman Birtaniya a Tarayyar Turai yace akwai babban kalubale, domin an fara gani tun daga faduwar darajar kudin kasar, kuma ficewar zai yi tasiri ga matsalar rashin ayyukan yi.

Tsohon Magajin garin London Boris Johnson yana daga cikin shugabannin yakin ficewa Tarayyar Turai kuma yanzu yana cikin wadanda ake ganin zasu gaji Firaminsita David Cameron.

Shugabannin manyan kasashen Turai da suka hada da Jamus da Faransa sun bayyana damuwa akan sakamakon zaben raba gardama da ya tabbatar da Birtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI