Turai- Birtaniya

Turai na son Birtaniya ta sanar da ita ficewarta

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Italiya sun bayyana cewar babu wata tattaunawa da za su yi da Birtaniya har sai ta sanar da su a hukumance kan aniyarta ta ficewa daga kungiyar kasashen Turai.

François Hollande na Faransa da  Angela Merkel ta Jamus da  Matteo Renzi na Italiya
François Hollande na Faransa da Angela Merkel ta Jamus da Matteo Renzi na Italiya John MACDOUGALL / AFP
Talla

Yayin wata ganawa da suka yi jiya kafin taron da shugabannin kasashen kungiyar 27 za su yi  a yau Talata, shugabannin sun bayyana aniyarsu ta gina kungiyar bayan ficewar Birtaniya.

Kasashen uku masu karfin fada aji cikin kungiyar ta tarayyar Turai sun bayyana cewa Britaniya yanzu ya dace ta yi aiki da doka ta 50 domin sabulewa daga cikin kungiyar, sannan ta tattauna batun harkan cinikayya da hulda da makwabtaka.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel mai masaukin baki a tattaunawa da Shugaban Faransa Francois Hollande da Fira Ministan Italiya Matteo Renzi a birnin Berlin ta bayyana cewa sun amince da fitar Birtaniya daga cikinsu, amma kuma akwai bukatar rubutacciyar wasika zuwa ga hukumar kungiyar Turai domin ta sani a hukumace.

Ministan kudi na Britaniya George Osboene tunda fari ya fadi cewa kasarsa za ta bi abinda doka ta 50 ta fadi ne kawai idan har ta hango inda kasar ta dosa da sauran kasashen kungiyar.

Shugabar gwamnatin Jamus ta fadi cewa babu wani lokaci da za a bata game da ficewar, sannan kuma za su duba dacewar matakan da za a dauka game da wasu kasashen da suka fara nuna bukatar ficewa daga wannan kungiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI