Faransa

An bude Masallaci a Faransa da ake takaddama a Nice

Masallaci da Makarantar En-Nour a Nice
Masallaci da Makarantar En-Nour a Nice VALERY HACHE / AFP

An bude wani babban Masallaci da Saudiya ta dauki nauyin ginawa a jiya Asabar a birnin Nice na Faransa bayan shafe shekaru 15 ana takaddama da mahukunta kan bude Masallacin.

Talla

Sai a jiya ne sabon magajin garin Nice ya bayar da umurnin bude Masallacin bayan ya gaji wanda ya turje kan kin amincewa a soma Sallah a ciki.

Tsohon magajin garin mai suna Christian Estrosi ya yi adawa ne da bude masallacin bayan ya zargi ministan harakokin addinin musulunci na Saudiya Sheikh Saleh bin Abdulaziz da kokarin yada Shari’a a Faransa.

Mutane 10 suka fara Sallah a masallacin mai daukar mutane sama da 800 wanda kotu ta bayar da umurnin a bude karkashin tsarin doka da ta ba Faransawa damar yin addinin da suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.