Spain

Hukuncin dauri na watanni 21 kan Messi da mahaifinsa

Messi da mahaifinsa a cikin zauren kotu
Messi da mahaifinsa a cikin zauren kotu REUTERS/Alberto Estevez/Pool/Files

A wannan laraba kotu ta yanke hukuncin dauri na tsawon watanni 21 akan shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi da mahaifinsa, saboda samun su da laifinyin coge wajen biyan haraji.

Talla

Hakazalika kotun ta bukaci mutanen biyu su biya tarar wasu kudade Euro milyan 3 da dubu 700 saboda wannan laifi da suka aikata tsakanin 2007 da 2009.

To sai dai an bai wa mutanen biyu damar daukaka kara a gaban kotun kolin kasar Spain.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI