Birtaniya

Theresa May za ta zama Firaministan Birtaniya

Theresa May Za ta zama sabuwar Firaministan Birtaniya
Theresa May Za ta zama sabuwar Firaministan Birtaniya REUTERS/Peter Nicholls

‘Yar Takarar shugabancin Jam’iyyar Conservatives a Birtaniya Andrea Leadsom ta janye, matakin da ya ba Theresa May zama ‘yar takara daya tilo wadda ke kan hanyar zama Firaministan kasar.

Talla

Firaminista David Cameron mai barin gado ya ce a ranar Laraba ne Theresa May za takarbi mukaminsa.

Cameron dai ya yi murabus ne bayan rashin nasara a zaben raba gardama da al’ummar Birtaniya suka zabi ficewa kungiyar Tarayyar Turai.

Janyewar takarar Andrea Leadsom ya zo wa yawancin al’ummar Birtaniya da mamaki ganin yadda a ‘yan kwanakin nan ta bukaci hadin kan al’ummar kasar wajen tabbatar da nasarar kasancewarta Firaminista.

A lokacin da ta ke sanar da matakinta na janyewa daga takarar, Leadsome ta ce Theresa May ita ta fi cancantar jan ragamar mulkin kasar ganin za ta iya gudanar da sauyin da kasar ke bukata a wannan lokacin da za ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai.

Theresa May mai shekaru 59 za ta kasance Mace ta biyu da ta taba rike mukamin Firaminista tun bayan Margret Thatcher .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI