Najeriya

Musulmai mata na rasa aiki a Turai saboda dan-kwali

Kamfanonin Turai na koran mata musulmai masu daura dan-kwali
Kamfanonin Turai na koran mata musulmai masu daura dan-kwali AFP PHOTO/ Shah Marai

Babbar kotun tarayyar Turai ta shiga tsaka mai wuya game da yanke hukunci kan haramta wa mata musulmai daura dan-kwali a bakin aiki kuma wannan na zuwa ne bayan wani babban alkalin kotun ya nuna rashin gamsuwarsa da matakin da kamfanonin Turai ke dauka na sallamar mata masu daura dan-kwalin.

Talla

Alkalin mai suna Eleanor Sharpston ya ce, rashin adalci ne wani kamafanin Turai ya hana ma’aikaciya musulma daura dan kwali a lokacin aiki.

Ra’ayin alkalin ya sha babban da wanda aka gabatar a baya kan wannan batu wanda ya goyi bayan haramta daura dan-kwalin.

A kwanan nan ne wani kamfanin sadawarwa da ke Faransa ya kori wata mata mai suna Asma Bougnaoui bayan ya yi korafi kan dan-kwalin da ta ke daurawa akanta.

Mr. Sharpston ya ce matakin da kamfanonin ke dauka tamkar nuna wariya ne ga matan.

Ko a watan Mayun da ya gabata sai da wani kamfanin samar da tsaro a kasar Belgium ya sallami wata Muslma bayan ta jajirce kan ci gaba da rufe kanta da dan-kwali.

Yanzu haka dai ya zama dole kotun ta yi nazari kan korafin da Mr. Sharpston ya yi kafin ta yanke hukuncin karshe kan batun.

Alkalin ya ce, bai ga dalilin da zai haramta wa Asma Bougnaoui gudanar da aikinta ba don kawai ta rufe kanta kamar yadda musulunci ya umarce ta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.