Poland

Jami'an tsaro dubu 40 za su kare Paparoma a Poland

Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya Paparoma Francis
Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya Paparoma Francis REUTERS/Tony Gentile

Gwamnatin Poland za ta girke jami’an tsaro fiye da dubu 40 domin bai wa shugaban mabiya darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis da mabiyansa kariya.

Talla

A cikin mako mai zuwa ne Paparoman zai ziyarci kasar ta Poland, inda zai gana da dubban matasan Katolika a bikin ranar matasa ta duniya.

Za a girke jami’an tsaron ne sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kaddamar a Faransa da Belgium da kuma Jamus, inda a jumulce mutane sama da 250 suka rasa rayukansu tun daga watan Janairun bara.

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.