Faransa

Gobara a mashaya ta kashe mutane 13 a Faransa

Ministan Harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve
Ministan Harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve BFM : Capture video

Mutane akalla 13 suka gamu da ajalin su, wasu 6 kuma suka jikkata sakamakon wata gobara data tashi safiyar yau Asabar a wata mashaya dake yankin Rouen, a arewacin Faransa.

Talla

Ministan harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve ya gaskata cewa cikin dare gobaran ta tashi yayin da ake wani buki, kuma masu aikin kwana-kwana akalla 50 suka yi ta aikin su domin kashe gobarar.

Acewar Ministan za’a gudanar da cikakken binciken musabbabin wannan gobara.

Wasu majiyoyi na cewa kyandir da aka kunna don ado a harabar bukin ya janyo gobarar.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.