Britaniya

Britaniya za ta jinkirta fita daga EU

Firaiyi Ministar Britaniya Theresa May
Firaiyi Ministar Britaniya Theresa May REUTERS/Peter Nicholls/File Photo

Firaminista Theresa May tace akwai alamar jinkirta ficewar kasar daga kungiyar kasashen Turai ganin yadda ma’aikata ke ta fafutuka da kuma zabubbukan da za’a gudanar a kasashen Faransa da Jamus.

Talla

Mrs Theresa May tace zata kaddamar da sharadi na 50 na yarjejeniyar kasashen Turai wanda zai baiwa kasar damar fara aiwatar da yarjejeniyar ficewa daga kungiyar a farkon shekarar 2017.

To amma rahotanni sun ce ministocinta sun gargadi manyan jami’an tattalin arziki a birnin London cewar hakan ba zai yiwu ba sai a karshen shekara ta 2019.

Wata majiya daga cikin jami’an da suka gana da ministocin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar ministocin na nazarin jirkita matakin har sai shekarar 2017.

Rahotan yace basu da kwararun jami’an da zasu gaba dan tattaunawa da jami’an kasahsen Turai, kuma ba suma san tambayar da ya kamata suyi ba.

Faransa zata gudanar da zaben shugaban kasa a watan Mayu na shekara mai zuwa yayin da Jamus zata gudanar da nata a watan Agusta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.