Faransa

Kotu ta dakatar da haramcin Burkini a Nice

Batun haramta sa kayan wanka a ruwa ya janyo muhawara a Faransa
Batun haramta sa kayan wanka a ruwa ya janyo muhawara a Faransa Reuters/Stringer

Kotu a birnin Nice da ke Faransa ta dakatar da haramci kan Sanya tufafin wanka a bakin teku, bayan hukumomin yankin sun yi watsi da hukunci da babbar kotun kasar ta yanke kan dokar ta Burkini.

Talla

Alkalai a birnin Nice, sun ce harin ranar 14 ga watan Yuli a wajen shakatawa da ke yanki bai bayar da hujjojin daukar matakin haramcin ba.

Hukuncin na zuwa bayan babban kotun kasar a makon da ya gabata, ta dakatar da haramci sanya tufafin na wanka a gabar teku a biranen kasar 30 da ke kudu maso gabashin Faransa da suka kafa dokar.

Birnin Nice da sauran yankunan kasar sun yi watsi da wannan hukunci kan Burkini da mata musulmi ke sanyawa, inda mahukunta jihohin ke ikirarin cewa barazana ce ga tsaro.

Kotun ta kuma ce amfani da tufafin na wanka da ake kira Burkini ba ya da wani hatsari ko jin kunya ko kariya a lokutan ninkaya.

Batun Burkini dai ya janyo muhawara tun hotunan da aka yada na wasu ‘yan sanda da aka nuna sun tursasawa wata mata cire mayafinta a gabar teku da kuma hoton bidiyo da ya nuna wani mai gidan abinci ya wulakanta wasu mata musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.