Isa ga babban shafi
Faransa

Wani Ma'aikaci da 'yan sandan Faransa suka fasa masa ido za shi Kotu

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Christophe Ena/Pool
Zubin rubutu: Garba Aliyu
1 Minti

A kasar Faransa wani dan kungiyar Kodago na shirin kai Rundunar ‘yan sandan Faransa kara saboda  yin sanadin ya rasa kwayan idon sa daya, yayin da ‘yan sanda suka ruffan masu, a lokacin da suke zanga-zangan lumana game da sabon tsarin kodago na kasar a farkon wannan mako.

Talla

Laurent Theron mai shekaru 46 ya fadi cikin tattaunawa dashi a wata tashar TV cewa zai shigar da kara kotu.

A cewar uwar kungiyar kodago dake Faransa shi wannan maaikaci, ‘yan sanda ne suka jefa masa gwangwanin hayaki mai sa kwalla, gwangwanin kuma ya fasa masa kwallon idon sa.

Tun cikin watan 7 daya gabata ne dai  kungiyoyin kodago a Faransa ke zanga-zanga jefi-jefi domin nuna adawa da sabon tsarin dokokin kodago na kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.