Isa ga babban shafi
Amurka

An gudanar da binciken ra'ayin jama'ar Amurka tsakanin Trump da Clinton

REUTERS/Jonathan Ernst
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Wani binciken kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya gudanar daga 23 zuwa 29 ga watan Satumba, ya nuna cewa ’yar takarar shugabancin Amurka karkashin Democrat Hillary Clinton, tana kan gaba wajen samun mogoya baya da kashi 5% fiye da abokin hamayyarta Donald Trump.

Talla

Sakamakon a zuwa bayan muhawarar farko daga cikin uku da zasu gudana tsakanin ‘yan takarar guda biyu.

Clinton na da goyon bayan kashi 43 yayinda Trump ke da kasha 38, a gefe guda kuma wasu mutanen kashi 19 suka ce babu wanda zasu goyawa baya cikin ‘yan takarar.

Idan har Hillary Clinton ta ashe zaben shugabancin kasar zata zama mace ta farko a tarihin kasar da ta dare kujerar shugabanci.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.