Isa ga babban shafi
Faransa

Dan Faransa na daga cikin ‘yan sama jannati da za su tafi duniyar sama

Thomas Pesquet dan kasar Faransa na daga cikin ayarin da za su duniyar sama.
Thomas Pesquet dan kasar Faransa na daga cikin ayarin da za su duniyar sama. REUTERS/Maxim Zmeyev
Zubin rubutu: Ramatu Garba Baba | Garba Aliyu
1 min

Thomas Pesquet na daga cikin ‘yan sama jannati da za su tafi duniyar sama wanda shine karo na farko cikin shekaru takwas da aka sami dan kasar Faransa a cikin ayarin ma su tafiya duniyar sama.

Talla

Thomas Pesquet dan shekaru 38 da sauran ‘yan sama jannatin za su tashi ne daga wata tashar tashi sama dake kasar Kazakhstan anjima kadan, a tafiyar watanni shida da za su yi.

Zai kasance dan kasar Faransa na 10 a tarihin tafiya duniyar sama, kuma mutun na farko da ya yi wannan tafiya daga Faransa cikin shekaru 8 da suka gabata.

Thomas Pesquet zai gudanar da jerin wasu bincike a tashar sama da za su taimakawa bil’adama.

Hukumar kula da sararin samaniya ta Turai wadda ke daukar dawainiyar tafiyar ta bayyana cewa ‘yan sama jannatin za su yi gwaje-gwaje da dama yayin zaman da za su yi a duniyar sama.

Kafofin yada labarai a Faransa sun yi ta yada wannan tafiya sama jannati da za a yi yau., tare da jinjinawa shi Thomas saboda hazakar sa da jajircewar wajen nazarin sararin samaniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.