Isa ga babban shafi
FIFA

Kotu ta yi watsi da bukatar Blatter

Tsohon shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter da Michel Platini tsohon shugaban UEFA
Tsohon shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter da Michel Platini tsohon shugaban UEFA
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Babbar kotun da ke sauraron kararraki kan wasanni, ta yi watsi da daukaka karar tsohon shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA Sepp Blatter, kan bukatar soke haramta mishi shiga sha’anin wasanni na tsawon shekaru shida.

Talla

A baya Sepp Blatter ya fuskanci wannan hukunci ne saboda samunsa da laifin biyan kudade da yawansu ya kai fan miliyan 2 ga Michel Platini, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta turai UEFA, ba bisa ka’ida ba.

Ko da yake Blatter ya bayyana rashin jin dadinsa game da wannan hukunci, ya ce a halin yanzu ya saduda da yunkurin da yake yi na ganin ya wanke kansa daga zargin almundahanar da ake masa.

Biyan makudan kudaden fan miliyan 2 da Blatter yayi ga Platini a shekarar ta 2011 ba bisa ka’aida ba, shi ne ya sabba daukar hukunci dakatar da shugabannin biyu; wanda a baya aka yi zaton cewa Platini ne zai maye gurbin Sepp Blatter a matsayin shugaban FIFA.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.