Faransa

Ko kun san wanene sabon Firaministan Faransa Cazeneuve

Sabon Firaiministan Faransa Bernard Cazeneuve
Sabon Firaiministan Faransa Bernard Cazeneuve

A yau talata ne shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya nada ministan cikin gida Bernard Cazeneuve a matsayin sabon Firaminista dan maye gurbin Manuel Valls wanda ya yi murabus don tsayawa  takarar shugabancin kasa a zaben shekara mai zuwa.

Talla

An haifi Bernard Cazeneuve a shekarar 1963, ya fito ne daga zura’ar mabiya jam’iyyar gurguzu a garin Oise, sannu a hankali tauraronsa ya dinga haskawa a fannin siyasar Fransa, inda a shekarar 1997 aka zabe shi dan majalisar dokoki kafin ya sake maimaitawa a 2002.

Tsohon dalibi ne da ya karanci ilimin kimiyar siyasa a jami’ar Bordeaux, ya kuma rike mukamin magajin garin Cherbourg a 2001 ya kuma ci gaba da rike mukamin aikin shara’a na yankin Normandy har zuwa 2012, lokacin da ya saka kafa a gwamnatin Jean-Marc Ayrault a matsayin ministan da ke kula da harakokin kasashen turai.

Duk da cewa a wancan lokaci Cazeneuve ba sananne ne ba a wurare da dama daga cikin Faransa amma ya ja ra’ayin shugaba François Hollande da mutanen da ke kewaye da shi, bisa yadda ya sadaukar da kansa a siyasance ta ko wane fanni, musamman sanayar da ya ke da ita ta siyasa wajen warware batutuwan da suka cije.

Cazeneuve wanda ya rike mukaman gwamnati da dama, ya taka mahinmiyyar rawa a fada da ayyukan ta’addanci a daidai lokacin da Faransa ke fuskantar matsalar tsaro da hare haren ta’addanci a kasar.

Makusantan shugaba Hollande, sun bayyana zaben Bernard Cazeneuve a kan mukamin Firaiminista a matsayin dai dai domin kuwa mutum ne da yake da kwarewa sosai, ta fannin tsaro da dubarun fada da ayyukan ta’addanci, ganin wannan lokaci da Faransa ke karkashin dokar ta baci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.