Faransa

Magajin Garin Faransa zai gurfana don kyamar Musulmai

Robert Ménard, Magajin Garin Béziers na Faransa
Robert Ménard, Magajin Garin Béziers na Faransa AFP PHOTO / SYLVAIN THOMAS

Majiyoyin shari’a na Faransa sun bayyana cewa, za a gurfanar da wani magajin gari da ya furta kamalan nuna kyama ga musulman kasar.

Talla

Robert Menard, wanda shi ne Magajin Garin Bezier kuma mai goyon bayan jam’iyyar National Front da ke adawa da baki, zai gurfana a gaban wata kotun birnin Paris saboda kalaman da ya yi na cewa, “ yawan Musulmai dalibai, babbar matsala ce a garinsa”

Mernard ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da kafar Channels LCI a ranar 5 ga watan Satumban da ya gabata, abin da ake ganin zai iya haddasa kiyayyar juna da kuma nuna banbanci.

Sai dai Magajin garin ya musanta cewa kalaman nasa na nuna banbanci ne ga wasu jama'a, in da ya ke cewa, kawai ya fadi halin da garinsa ke ciki ne.

Kungiyar LICRA da ke yaki da nuna wariya a Faransa, ta bayyana cewa, a ranar 8 ga watan Maris mai zuwa ne za a gurfanar da Magajin Garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.