Mutane 37 sun mutu a hadarin jirgin Turkiya

Faduwar Jirgin dakon kaya na Turkiya a Kyrgyzstan
Faduwar Jirgin dakon kaya na Turkiya a Kyrgyzstan REUTERS

Akalla mutane 37 suka mutu da suka hada da yara kanana bayan faduwar wani jirgin sama mai dakon kaya na Turkiya kusa da filin saukar jirgin Bishkek babban birnin kasar Kyrgyzstan.

Talla

Hukumomin lafiya a Kyrgyzstan sun ce mutanen yankin da jirgin ya fadi ne suka fi mutuwa kuma cikinsu akwai yara kanana guda 6. Sannan matukan jirgin guda hudu ne suka mutu.

Faduwar jirgin kuma ya lallata gidaje akallla 43 a kauyen Datcha Souou da ya fadi. Rahotanni sun ce kuskure daga matukun jirgin ne ya yi sanadin faduwar jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.