Amurka

Tarihin sabon shugaban Amurka Donald Trump

Sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump a lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki.
Sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump a lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki. CHIP SOMODEVILLA / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

A yau Juma'a Donald Trump ya karbi ragamar mulkin shugabancin Amurka a cikin wani yanayi na rashin kwarewa a siyasa da diflomasiyya da sanayyar aikin soji a wannan kasa mafi girma a siyasa da kuma tattalin arziki a duniya.

Talla

Donald John Trump hamshakin attajirin Amurka ne da ya yi suna a shirinsa na tilibijin

A shekarar 1946 aka haifi Trump a birnin New York kuma ya yi karatun digirinsa ne a fannin nazarin tattalin arziki a Jami’ar Pennsylvania a shekarar 1968.

Trump ya gaji arziki ne daga kamfanin iyayen shi Elizabeth Trump and Sons na hada-hadar gidaje da gine-gine wanda ya yi ficen gina dogayen benaye da otel otel da gidajen caca da kuma filayen wasan kwallon golf.

Donald Trump dai shi ne mutum na 113 a jerin attajiran Amurka

A shekarar 2000 ya fara shiga siyasa, kuma ya canza sheka daga Jam’iyyar Democrat zuwa Republican.
Trump ya fara yakin neman zaben 2016 da duniya ke kallo kamar almara saboda salon siyasar shi na fadin duk abin ya fito bakin shi.

Da haka kuma Trump ya doke Hillary Clinton ‘yar democrat.

Trump mai shekaru 70 a duniya shi ne shugaba na farko mai yawan shekaru da aka rantsar a Amurka, Kuma shugaban Amurka na farko da bai taba rike mukamin siyasa ba.

Donald Trump yana da mata guda da ‘ya’ya biyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.