Amurka

Trump ya bada umurnin sauya shirin Obamacare

Sabon Shugaban Amurka Donald Trump
Sabon Shugaban Amurka Donald Trump JOE RAEDLE / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

A karo na farko bayan fara aikinsa a matsayin shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan umarnin gudanar da sauyi kan shirin lafiya na Obamacare.

Talla

Tun a yayin yakin neman zabensa, Trump ya bayyana aniyarsa ta soke tsarin kula da lafiyar na Obamacare, wanda ya ce yana cike da kura kurai.

Zalika sabon shugaban kasar tuni ya bada damar sauya tsarin shafin Internet na fadar White House tare da bada umurnin sauya manufofin gwamnatin Barrack Obama da ta shude, bisa canjin yanayi.

Sabon shugaban Amurkan na 45, Donald Trump da aka rantsar jiya juma’a, yayi alkawarin fifita muradun kasar fiye da komai, wanda ya tabbatar cikin jawabin da ya gabatar jim kadan bayan rantsar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI