Faransa

Faransa: Hamon ya tabka muhawara da Valls

'Yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar gurguzu Benoît Hamon  Manuel Valls
'Yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar gurguzu Benoît Hamon Manuel Valls REUTERS/Bertrand Guay

Dan Takaran shugabancin Faransa Benoit Hamon ya bukaci masu kada kuri’a da su goyi bayan shirinsa na farfado da kasar da ya ce zai daga kimarta a idon duniya.

Talla

Hamon na jawabi ne a mahawarar karshe da suka gudanar da Manuel Valls kafin zaben fidda gwani da za a yi a karshen wannan mako.

A mahawarar da suka tafka daren jiya, Benoit Hamon ya bukaci masu kada kuri’a da su kaucewa goyan bayan tsoffin da ke mulkin kasar, wadanda ya ce sun kasa kawo sauyin da ake bukata.

Hamon mai shekaru 49 ya bayyana kan sa a matsayin dan takarar sauyi wanda ke dauke da sabbin dabarun da suka hada da inganta albashin ma’aikata da bai wa dattijai kudin kashewa da kuma kare muhalli.

Hamon ya ce zai dora haraji kan mutum mutumin da aka da su a kasar da halatta zukar tabar wiwi da haramta amfani da kayan da ake hada su sinadarai masu guba da kuma kafa wata rundunar da za ta yi yaki da masu nuna banbanci.

A na shi bangaren Manuel Valls ya bayyana Hamon ne a matsayin dan takaran da ke ci gaba da mafarki kuma wanda bai san yadda duniya take ciki ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.