Faransa

'Yar Faransa ta zama sarauniyar Kyau a duniya

'Yar Faransa Iris Mittenaere ce ta ci sarauniyar Kyau a bana.
'Yar Faransa Iris Mittenaere ce ta ci sarauniyar Kyau a bana. REUTERS/Erik De Castro

Iris Mittenaere ta lashe kyautar Sarauniyar kyau ta wannan shekarar da aka gudanar a birnin Manilla da ke kasar Philippines.

Talla

Mittenaere mai shekaru 24 ta doke ‘Yar kasar Haiti da Colombia wadanda suka zo na biyu da na uku wajen samun nasara daga cikin mata 85 da suka shiga gasar.

Sabuwar Sarauniyar kyaun ta Duniya ta yi bayani kan muhimmancin karbar bakin da ke gujewa kasashen da ake samun rikici.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.