Faransa

Sarkozy zai fuskanci Shari'a a Faransa

Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa
Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa REUTERS/Ian Langsdon

Wani babban Alkali a kasar Faransa ya bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy kan badakalar kudaden yakin neman zabensa a shekarar 2012.

Talla

Ana zargin Sarkozy da Jam’iyyarsa ta UMP da boye wasu kudaden yakin neman zaben shi da suka kai kudi euro miliyan 18.

Amma tsohon shugaban na Faransa ya musanta zargin inda ya ce ba ya da masaniya game da kashe kudaden da suka zarce adadin wadanda aka ware domin yakin neman zabensa.

Lauyan da ke kare Sarkozy, Thierry Herzog ya ce za su daukaka kara domin kalubalantar matakin na kotun.

Sarkozy dai ya sha kaye a zaben 2012 da aka gudanar wanda shugaba na yanzu Francois Hollande ya lashe.

Dokokin Faransa sun sanya iyaka kan yawan kudaden za a iya kashewa yayin yakin neman zabe. Sai dai bayanai sun ce Jami`yyar UMP ta Sarkozy ta kashe kudaden da suka zarce adadi ta hanyar kawance da wani kamfani da ake kira Bygmalion.

Tuni dai wasu daga cikin ma`aikatan kamfanin na Bymalion suka amsa cewa tabbas wannan badakala ta auku tsakaninsu da Jam`iyyar UMP ta Sarkozy, kuma a halin da ake ciki an fara bincikar wasu manyan kusoshin jam`iyyar da dama.

Mista Sarkozy shi ne tsohon shugaban Faransa na biyu da ya ke fuskantar shari`a tun daga shekara ta 1958.

A shekara ta 2011 aka yankewa tsohon shugaban kasar Jacques Chirac hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyu saboda fasaka da kudin al`umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.