Wasanni

An tsawaita wa`adin haramtawa Rasha shiga wasannin motsa jiki

Rune Anderson shugaban kamitin sa`ido kan da`a a wasannin motsa jiki, na hukumar shirya wasannin ta duniya IAAF
Rune Anderson shugaban kamitin sa`ido kan da`a a wasannin motsa jiki, na hukumar shirya wasannin ta duniya IAAF

Kwamiti na musamman da ke sa`ido kan tabbatar da da`a na karkashin hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya IAAF, ya ce haramcin da aka kafawa `yan wasan motsa jiki na kasar rasha zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Nuwamba na shekarar da muke ciki.

Talla

Shugaban kwamitin sa`idon Rune Anderson ya sanar da haka yayin zantawa da manema labarai, wanda hakan ke nuni da cewa kasar Rash aba zata halarci gasar wasannin motsa jiki ta duniya da za`ayi ba watan Augusta a birnin London.

Tun a watan Nuwanban shekara ta 2015 aka haramtawa `yan wasan Rasha da dama shiga wasannin motsa jiki, bayan rahoton da Hukumar yaki da shan kwayoyin Karin kuzari WADA mai zaman kanta ta wallafa na zargin gwamnatin Rasha da goyon bayan `yan wasanta wajen shan kwayoyin.

A shekarar 2016 da ta gabata aka sake tabbatar da haramcin kan Rasha, wanda hakan yasa mafi yawancin `yan wasan Rasha suka gaza shiga gasar Olympics da ta gudana a birnin Rio na Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.