Mexico

Dubban 'yan Mexico sun nuna fushinsu kan Trump

Dubban mutane a Mexico da ke zanga zangar tur da shugaban Amurka Donald Trump
Dubban mutane a Mexico da ke zanga zangar tur da shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jose Luis Gonzalez

Dubban ‘yan kasar Mexico ne suka shiga wata zanga zangar da akayi a Mexico-City don nuna fushinsu kan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ke dauka na tirsasawa kasar korar baki da kuma dakile harkokin kasuwanci.

Talla

Masu zanga zangar sun dauki wani katon allo dake dauke da rubutun dake nuna cewar, dole a mutunta Mexico, yayin da suke daga tutar kasar.

Daya daga cikin masu zanga zangar, Juliet Rosas ya ce, bukatarsu itace nunawa Trump cewa kasar Mexico a hade take, kuma manufofinsa ba za suyi tasiri kansu ba.

Akalla mutane 20,000 ne suka shiga zanga zangar, banda wadanda akayi a garuruwan Guadalahara da Monterrey da Moreila da ke kasar.

A gefe guda kuma wasu daga cikin ‘yan kasar ta Mexico sun rika fadin munanan kalamai kan shugaban kasar Enrique Pena Nieto, a matsayin jagoran da ya kasa yin komai wajen kawo karshen matsalar cin hanci da rashawa da ta yiwa kasar katutu, sai kuma kasa warware fadace fadacen da ke aukuwa a wasu sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.