Amurka

An karrama bakar fata a Gasar Oscar

Jaruman fina-finan Hollywood da suka lashe kyaututuka.
Jaruman fina-finan Hollywood da suka lashe kyaututuka. REUTERS/Lucas Jackson TPX IMAGES OF THE DAY

Viola Davis ta lashe kyautar bikin karrama gwarzayen fina-finan Hollywood da aka kammala dazu a Amurka saboda gudummawar da ta bayar a shirin fim din Fences, inda ta taka rawa a matsayin matar auren da mijin ta ke gallaza mata.

Talla

Wannan ne kyauta na uku da ta lashe saboda rawar da ta taka, bayan kyautar Golden Globe da Screen Actors Guild.

Wannan ya nuna sauyi akan bikin bara wanda babu wani bakin fata da ya samu kyautar.

Wasu daga cikin wadanda suka samu kyaututuka sun hada da ‘The Best Salesman’ da wani dan kasar Iran ya shirya amma aka hana shi zuwa Amurka wajen bikin, sai kuma ‘Zootopia’.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI