Tarayyar Turai

An bukaci karin kudade don mayar da ‘Yan gudun hijra kasashensu

Tarrayar Turai ta bukaci karin kudade don mayar da 'Yan gudun hijra da ke jibge a Libya kasashensu.
Tarrayar Turai ta bukaci karin kudade don mayar da 'Yan gudun hijra da ke jibge a Libya kasashensu. (©Reuters)

Shugaban Kungiyar kasashen Turai ya bukaci kungiyar ta kara kudaden da take bai wa hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya dan mayar da baki ‘yan kasashen Afirka ta suka makale a kasar Libya.

Talla

Kasar Malta da ke shugabancin kungiyar ce ta gabatar da bukatar kafin taron shugabanin kungiyar da za’ayi a makon gobe.

Hukumar kula da mutanen dake kaura ta ce yanzu haka akwai baki tsakanin 700,000 zuwa miliyan guda a Libya, wadanda suka shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi, kuma suna bukatar komawa kasashen su.

Malta ta bukaci kasashen da ke kungiyar da su taimaka dan mayar da wadannan baki da ke mutuwa a tekun kasashen su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.