Amurka

Trump ya bayyana goyon bayansa ga NATO

Trump ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar kawancen tsaro ta NATO
Trump ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar kawancen tsaro ta NATO AFP/ GEORGES GOBET

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya jaddada goyan bayan sa ga kungiyar kawancen tsaro ta NATO amma ya ce dole kasashen dake kungiyar su biya kudaden tafiyar da ita domin ba hakkin sa bane ya wakilci kasashen duniya.

Talla

A jawabin sa na farko ga taron Majalisar kasar, shugaban ya ce aikin dake gaban sa shine wakiltar Amurka da manufofin ta, duk da yake ya na goyan bayan kungiyar tsaron.

Shugaba Trump yayi alkawarin ware Dala triliyan guda dan gina kayan more rayuwa a fadin kasar, inda yake cewa Amurka ta kashe abinda ya kai triliyan 6 a Gabas ta Tsakiya maimakon amfani da kudin dan sake gina kasar.

Trump ya kuma bayyana shirin kawo sauyi a harkar karbar haraji a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.