Faransa

Fitattun 'yan siyasa a Faransa na janyewa daga tafiyar takarar Fillon

Dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Republican François Fillon.
Dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Republican François Fillon. Christophe ARCHAMBAULT / AFP

Wasu dake kan gaba a kwamitin yakin neman zaben Francois Fillon don shugabancin kasar Faransa sun sun fice daga kwamitin.

Talla

Jami’an yakin neman zaben dai sun ce Fillon ya saba alkawarin da ya dauka cewa zai janye daga takara matukar kotu ta tuhume shi da aikata ba daidai ba, kan batun bai wa matarsa albashi mai tsoka bisa aikin da bata gudanar ba.

Wata sanarwa daga kotun dai na nuni cewa mai dakin Fillon, Penelope za ta bayyana a gaban alkalai nan gaba kadan domin amsa wasu tambayoyi kan zargin da ake mata.

Tuni dai wasu daga cikin fitattu a fagen siyasar Faransa dake tafiya da Mista Fillon suka soma zamewa daga Goyon bayan da suke masa, ciki kuwa harda, Bruno Le Maire, Jean Christophe Lagarde.

Yan siyasar na kallon dan takarar jam’iyyar ta Republican a matsayin wanda ya kaucewa alkawarin da ya dauka a baya, cewa mudin kotu ta tuhume shi bisa zargin da ake masa to zai janye takararsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.