Fitaccen dan wasan Faransa Raymond Kopa ya rasu
Wallafawa ranar:
Fitaccen tsohon dan wasan Faransa Raymond Kopa ya rasu a yau Juma’a yana da shekaru 85 a duniya. Ya rasu ne bayan shafe lokaci mai tsawo yana jinya.
Kopa tsohon dan wasan Real Madrid ne da ya lashe kofunan Turai uku a wajajen 1950 da yanzu da ake kira gasar zakarun Turai.
Ana ganin Kopa ne ya fara fice a duniyar kwallon kafa a Faransa kafin bayyanar Michel Platini da Zinedine Zidane Thierry Henry da Paul Pogba.
Hukumar wasannin Lig a Faransa ta ce za a ware tsawon minti guda domin karrama tsohon dan wasan a dukkanin Lig Lig din kasar.
Kopa ya taba zama garzon dan wasan duniya a 1958, a shekarar da suka fitar da Pele na Brazil a gasar cin kofin duniya zagayen kusa da karshe.
‘Yan wasa da dama n ke ta bayyana alhinin rashin tsohon fitaccen dan wasan wanda ya jefa wa Faransa kwallaye 18 a wasanni 45.
Kopa da ke buga tsakiya ya kuma ci wa Real Madrid kwallaye 30 a wasanni 103.
Shugaba Hollande na Faransa ya danganta Kopa a matsayin wanda Faransa ba za ta taba mantawa da shi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu