Faransa

An gudanar da taron nuna goyon baya ga Fillon a Paris

Tsohon Firaministan Faransa kuma dan takarar shugabancin kasar Francois Fillon, yayinda yake jawabi ga magoya bayansa a birnin Paris.
Tsohon Firaministan Faransa kuma dan takarar shugabancin kasar Francois Fillon, yayinda yake jawabi ga magoya bayansa a birnin Paris. REUTERS/Philippe Wojazer

Dan takarar shugabancin Faransa jam’iyyar Republican Francoise Fillon ya bukaci magoya bayansa da su cigaba da marawa takararsa baya.

Talla

Fillon yayi wannan kiran ne, yayin da ya gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa, da suka gudanar da gagarumin tattaki don nuna masa goyon baya.

Ana dai kallon taron da aka gudanar a birnin Paris a Matsayin zakaran gwajin dafin nuna farin jinin Francois Fillon, yayinda shugabannin jam’iyyarsa ta Republican, ke matsa lambar ya janye takararsa, bisa zargin aikata ba dai dai ba, na biyan matarsa Penelope albashin da bata cancanta ba.

Tun bayan bullar wannan zargin dai, Fillon na cigaba da fuskantar dusashewar farin jininsa, tsakanin ‘yan takarar neman shugabancin Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.