Faransa

Penelope Fillon ta maida martani kan zargin da ake wa maigidanta

A karon farko Penelope Fillion uwargidan dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam’iyyar Republican Francois Fillon, ta maida martani kan zargin da ake yiwa maigidanta game da aikata ba dai dai ba.

Uwargida Penelope da maigidanta Francois Fillon dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Repulican
Uwargida Penelope da maigidanta Francois Fillon dan takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Repulican REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Cikin hirar da ta yi ta farko, tun bayan zargin da fara, na cewa ta karbi albashin euro 900,000 daga maigidanta Fillon tsohon firaministan Faransa, Penelope ta shaidawa jaridar Le Journal Du Dimanche cewa, albashin halalinta ne, don kuwa ta yi ayyukan da ta cancanci albashin.

Zalika Penelope ta bukaci mai gidan nata Fracois Fillon da ya ci gaba da taka takara, har sai sunga abinda hali zai yi.

Zargin da ake yiwa Fillon na bai wa matarsa da ‘ya’yansu guda biyu aiki a majalisar Faransa yayinda yake Firaministan kasar, na cigaba da jawo dusashewar farin jininsa a tsakanin 'yan takarar shugabancin Faransa, inda zuwa yanzu wasu na hannun damansa suka janye daga yakin neman zabensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI