Amurka

Tony Blair ya musanta cewa Trump zai dauke shi aiki

Tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair.
Tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair. REUTERS/Stefan Rousseau/Pool

Tsohon firaminstan kasar Birtaniya Tony Blair, ya karyata rahotannin da ke cewa ya gana da na hannun dama kuma sirikin shugaban Amurka Donald Trump don daukarsa aiki. 

Talla

A baya wata jarida da ake wallafawa a Amurka ta fitar labarin cewa Tony Blair ya gana da surikin Trump Jarde Kushner, a satin da ya gabata don zama mai bai wa trump shawara kan yankin gabas ta tsakiya, kuma ganarwasu ta 3 kenan tun daga watan Satumban shekarar bara.

Da fari dai mai Blair bai fitar da wata sanarwa da ke karyata hakan ba.

To sai dai a Lahadinnan wani mai magana da yawunsa, ya ce babu gaskiya cikin labarin ballantana tushe ko makama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.