Faransa

Fillon ya ki janye takararsa a Faransa

François Fillon Dan takarar Jam'iyyar Republican a Faransa
François Fillon Dan takarar Jam'iyyar Republican a Faransa France 2

Dan takarar jam’iyyar Les Republicains a zaben shugabancin Faransa Francios Fillon yak i jingine takararsa duk da matsin lamba da yak e fuskanta daga bangaren jam’iyyarsa sakamakon zargin ya bai wa iyalansa aiki ba tare da ya bin ka’ida ba.

Talla

Fillon ya shaidawa magoya bayansa a gangamin yakin neman zabensa a dandalin Trocadero arewacin Paris cewa ka da su ja da baya.

Sai dai a karon farko dan takarar ya nemi jama’a gafara sakamakon bai wa matarsa Penelope aiki a matsayin mataimakiyarsa lokacin da ya ke rike da mukamin dan majalisa.

"Ya zaman wajibi in nemi gafara domin kare mutunci na da na matata, daga nan kuma sauran aiki ya rataya a wuyanku domin kare muradun kasarmu", a cewar Fillon.

Fillon ya amsa cewa Lalle ya aikata kuskure wajen bai wa matar shi aiki, amma ya ce ya yi haka ne saboda tunanin kwararra ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.