Jam'iyyar Republican ta sabunta goyon bayanta ga takarar Fillon
Wallafawa ranar:
Dan takarar neman kujerar shugabancin Faransa karkashin jam’iyyar Republican Francois Fillon, ya samu goyon bayan baki dayan ‘ya’yan jam’iyyarsa game da cigaba da taka takara.
‘Yan jam’iyyar ta Repuclican sun cimma wannan matsayar ce, bayan zaman tattaunawar kwamitin zartawar jam’iyyar domin tattauna kalubalen da suke fuskanta dangane da zargin da ake yiwa dan takarar tasu na sabawa doka ta hanyar biyan matarsa Penelope albashin da bata cancanci ta karba ba.
Yayin zaman ne dai ilahirin jiga jigan jam’iyyar ta Republican suka sabuta goyon bayansu ga takarar Fillon.
A baya dai Fillon ya fuskanci matsin lamba daga ‘yan jam’iyyar da dama, kan ya janye takararsa, inda har wasu ke ganin tsohon firaministan Faransa Alain Juppe ya maye gurbin takarar ta Fillon, sai dai kuma Juppe ya bayyana cewa a kai kasuwa.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai, dubban magoya bayan Fillon suka gudanar da taron nuna goyon bayansu ga takararsa a birnin Paris, inda Fillon ya shaida musu cewa zai cigaba da taka takara babu ja da baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu