Amurka-Iraqi

Trump ya cire 'yan Iraqi daga wadanda ya haramtawa shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jim Lo Scalzo/Pool

Gwamnatin Amurka ta cire kasar Iraqi daga cikin jerin kasashen Musulmi 7 da shugaban kasar Donald Trump ya bada umarnin haramtawa ‘yan kasar shiga Amurka.

Talla

Jim kadan bayan fitar da sanarwar, gwamnatin Iraqi ta yabawa Donald Trump bisa matakin da ya dauka na cire kasar ta Iraqi daga jerin wadanda aka haramtawa yan kasar shiga Amurka.

Ma’aikatar harkokin waje ta Iraqi ta ce matakin yana da muhimmanci wajen sake karfafa dangantakar kasashen biyu.

Dokar hana baki da kuma Musulmi shiga Amurka daga kasashen Musulmi 7 da suka hadar da Syria, Somalia, Iran, Iraqi, Yemen, Sudan da kuma Libya, da shugaban Amurka Donald Trump ya sanyawa hannu ta jawo gagarumar zanga zanga biranen Amurka da kuma wasu manyan biranen kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI