Hungary

Hungary ta dauki matakan dakile kwararar baki

Dubban 'Yan gudun hijira sun kafa sansani a Horgos kan iyakar Hungary da Serbia
Dubban 'Yan gudun hijira sun kafa sansani a Horgos kan iyakar Hungary da Serbia REUTERS/Marko Djurica

Majalisar dokokin Hungry ta amince da wata doka da ke bayar da umurnin kama bakin da suka shiga kasar ta barauniyar hanya. Firaministan kasar Viktor Orban ya ce daukar matakin zai taimaka domin kara tabbatar da tsaro a Yankin Turai.

Talla

A shekara ta 2013 ne kasar Hungary ta fara daukar irin wannan mataki domin hana baki musamman wadanda ke fitowa daga Syria shiga kasar, matakin da aka soke sakamakon matsin lambar kungiyar Turai da kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

A Karkashin dokar, duk wanda ya shiga kasar ba kan ka’ida ba to za a tsare shi a wani sansani na musamman sai zuwa lokacin da aka fayyace makomarsu. Yayin da wani bangaren na dokar ke cewa wadanda ba a tantance ba za su dauki nauyin mayar da kansu zuwa kasashensu.

Sau da dama Firaministan kasar Viktor Orban na bayyana bakin da ke neman shiga kasar a matsayin wani ayari na ‘yan ta’adda.

Sai dai hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana dokar a matsayin wadda aka kafa domin cin zarafin bil’adama musamman mata da kananan yara wadanda ko da yaushe ke cikin ayarin bakin da ke neman shiga kasar a hanyarsu ta zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.