Turai

An sake zaben Donald Tusk a kujerar Shugabancin kungiyar Turai

Donald Tusk Shugaban kungiyar Tarrayar Turai
Donald Tusk Shugaban kungiyar Tarrayar Turai REUTERS/Yves Herman

An sake zaben Donald Tusk na kasar Poland a matsayin sabon Shugaban kungiyar Tarayyar turai a wa’adi na biyu.

Talla

Donald Tusk da ya fuskanci barazana daga kasar sa Poland ,wacce ta yi gargadin kauracewa taron kungiyar muddin aka sake zaben Mista Tusk,
ya samu goyon bayan manyan kasashe masu karfin fada a ji, kamar kasar Jamus da ta ce rashin sake zaben Tusk illa ne ga ci gaban Tarrayar Turai musamman kan batun ficewar Birtaniya daga kungiyar.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce sake zaben Donald Tusk a matsayin shugaban Tarayyar Turai, shi zai tabbatar da dorewar kungiyar duk da adawa da Mista Tusk ke fuskata daga bangaren kasar sa Poland.

Shugabannin Turai nada hurumin ganin Donald Tusk ya taka muhimmiyar rawa ga dorewar Tarayyar turai musamman kan rawar da zai taka ga tattaunawar ficewar Birtaniya a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.