Turkiya-Netherland

Turkiya ta shiga takun-saka da Netherland

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Murad Sezer

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya shiga takun-saka da Netherland bayan hana manyan ministocinsa gudanar da gangami kan zaben raba gardamar da zai fadada karfin ikon sa.

Talla

Erdogan ya ce ''Ya zama dole mu koyawa Netherland cewa Diflomasiya ba abin wasa ba ce''.

Turkiya na ci gaba da tashin hankali da kawayenta na Tarayyar Turai kan bukatar manyan jami’an gwamnatin Erdogan na gudanar da gangami a ketare kan zaben raba gardamar da za a kada 16 ga watan Afrilu, don sauya kudin tsarin mulkin kasar, da zai karawar shugaban karfin mulki.

Sai dai Sabon rikicin da ke kunon kai tsakanin Turkiya da Netherland na neman kasancewa mafi tsanani a yanzu, inda shugaba Erdogan ya fito yana ambatar sunan kasar cewa ''idan Netherland ta shirya sadaukar da alakar da ke tskaninmu kan wannan zabe to tabbas zata ji a jikinta domin bashi ta dauka’’.

An dai kora iyalan Ministar Erdogan, Fatma Betul Sayan kaya, daga Netherland bayan hanata yin jawabi a gangami da aka tsara gudanarwa a Rotterdam da ke kasar.

Batun da Turkiya ke cewa Ministar da Tawagarta sun fuskanci wulakanci da Bazasu bari ya wuce haka nan ba.

Wannan rikici na zuwa ne bayan kace-nace da aka samu tsakanin Turkiya da Jamus kan gudanar da irin wannan taro a kasar.

Masu sharhi na hasashen a samu kuri’a kai da kai a zaben da za a gudanar, yayin da manyan ministocin kasar ke shirin aiwatar da gangami a manyan biranen tarayyar Turai don samun kuri’a daga miliyoyin turkawa da ke zaman ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI