Turkiya

Erdogan ya soki Merkel

Shugaban Kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya zargi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da goyan bayan ta’addanci, yayin da rashin jituwar da ke tsakaninsu ke ci gaba da tabarbarewa.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan AFP
Talla

Erdogan ya ce sun aike da takardun bayanai mai dauke da shafuna 4,500 a Jamus akan wasu ‘yan Turkiya da ake zargi da ayyukan ta’addanci amma Jamus ta ki mika su domin fuskantar shari’a.

Shugaban ya ce kin mika Kurdawan da ake zargi da laifufukan da suka shafi ta’addanci kamar goyan bayan abinda suke yi ne.

Wannan na zuwa a yayin da Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi shugaba Erdogan, da ya kaucewa matakan da za su lalata alakar kasarsa da su.

A makon da ya gabata Erdogan ya zargin cewa Holland na yanayi da gwamnatin Nazi, bayan da kasar, ta hana ministocinsa gudanar da taron nuna goyon bayan karawa shugabancinsa karfin iko da suka shirya a kasar.

Babbar jami’ar diflomasiyar Turai Federica Mogherini ta yi gargadi ga Turkiya ta kaucewa furta kalaman da za su kara dagula dangantakar da ke tsakaninsu.

Turkiya yanzu na barazanar warware yarjejeniyar takaita ‘yan gudun hijira da ta kulla da Tarayyar Turai da nufin amincewa da ita a matsayin mamba a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI