Turai

Kamfanoni a Turai sun samu ‘yancin haramtawa Mata sa hijabi

Faransa ta haramtawa mata lullebe fuska a bainar jama'a
Faransa ta haramtawa mata lullebe fuska a bainar jama'a REUTERS/Gonzalo Fuentes

Babbar kotun Turai a Luxemburg ta ce kamfanoni masu zaman kansu na iya haramtawa mata saka tufafin da ke nuna addini ko siyasa wanda ya kunshi matan musulmi da ke sa hijabi.

Talla

Hukuncin kotun na zuwa bayan wani kamfani a Belgium ya kori wata mata musulma saboda ta dage kan sai ta saka hijabi a wajen aikinta.

Babbar kotun ta Turai tace dokokinta ba za su yi karo da dokokin da kamfanoni suka shata ba, don haka idan akwai doka da kamfani ya kafa da ke haramta saka hijabi ba laifi ba ne.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana adawa da matakin wanda ta ce zai kara bude kofar cin zarafin mata musulmi.

Batun saka hijabi dai na ci gaba da janyo cece-kuce a Turai musamman daga bangaren masu kishin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.