Faransa da Jamus sun gargadi Erdogan na Turkiyya
Wallafawa ranar:
Shugaban Faransa Francois Hollande da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel sun bayyana kalaman Racep Tayyep Erdogan na Turkiyya da ke bayyana gwamnatocin Jamus da Netherlands a matsayin masu koyi da ‘yan Nazi da cewa hakan bai dace ba
Shugabannin biyu sun bayyana haka ne a wata sanarwar hadin-gwiwa da suka fitar a bayan tattauwa ta wayar tarho a yau alhamis cewa, ba za a iya lamunce wa irin wannan furuncin na Erdogan ba.
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya shiga takun-saka da Netherland bayan hana manyan ministocinsa gudanar da gangami kan zaben raba gardamar da zai fadada karfin ikon sa.
Erdogan ya ce ''Ya zama dole mu koyawa Netherland cewa Diflomasiya ba abin wasa ba ce''.
Turkiya na ci gaba da tashin hankali da kawayenta na Tarayyar Turai kan bukatar manyan jami’an gwamnatin Erdogan na gudanar da gangami a ketare kan zaben raba gardamar da za a kada 16 ga watan Afrilu, don sauya kudin tsarin mulkin kasar, da zai karawa shugaban karfin mulki.
Sai dai Sabon rikicin da ke kuno kai tsakanin Turkiya da Netherland na neman kasancewa mafi tsanani a yanzu, inda shugaba Erdogan ya fito yana ambatar sunan kasar cewa ''idan Netherland ta shirya sadaukar da alakar da ke tskaninsu kan wannan zabe to tabbas zata ji a jikinta domin bashi ta dauka’’.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu